Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Murnar Nasarar Janar Buhari daga Kebbi, Sokoto zuwa Zamfara


Murnar nasarar Janar Buhari a Sokoto

Da sanar da sakamakon zaben jihar Delta jama'a suka yi ca akan tituna suna murna

Yayinda wasu suke wasa da ababen hawa wasu ko suna fasa tukwane da ruwa duk a yin bikin murnar da Janar Buhari ya samu.

Mutane sun bayyana jin dadinsu da suka kwatanta da sauke faralin zuwa Makka. Sun ce abun da suka sha nema fiye da shakaru goma sha shida sai wannan karon Allah Ya tabbatar. Sun ce sun roki Allah Ya basu mutum adali kuma ya basu. Fatansu yanzu shi ne Allah ya taimaki sabon shugaban. Allah ya sa shi Janar Buhari ya yi adalci yadda 'yan Najeriya suka yi masa adalci suka zabeshi.

Duk da girke dakarun tsaro dauke da makamai hakan bai hana mutane yin dafifi ba a tituna tare da yin tafi da wake-wake. Wani abun mamaki ma shi ne yadda wasu jami'an tsaro suke nuna tasu murnar.

Lamarin ma haka yake a jihohin Kebbi da Zamfara inda dubun dubatan jama'a suka fito suka yi dafifi akan titunan biranen Gusau da Birnin Kebbi saboda nuna farin cikinsu akan nasarar Janar Buhari.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG