Zan Ba Gwamnatin Jonathan Maki kasa da Hamsin-Prof Zalanga

Professor Samuel Zalanga

Wani mai ilimin rayuwar dan adam da zamantakewa, Professor Samuel Zalanga, kuma mai sharhi kan lamura ya bayyana cewa, gwamnati mai barin gado ta gaza biyan muradun jama’ar da suka dorata bisa karagar mulki

An bayyana aikin da gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta gudanar cikin shekaru shida da suka shige a matsayin wadda ta sami makin ba yabo- ba fallasa.

Wani mai ilimin rayuwar dan adam da zamantakewa, Professor Samuel Zalanga, kuma mai sharhi kan lamura ya bayyana cewa, gwamnati mai barin gado ta gaza biyan muradun jama’ar da suka dorata bisa karagar mulki. Yace akwai abubuwa da daman a jin dadin rayuwa da al’umma ke bukata idan za a yi la’akari da irin ci gaban da aka samu a duniya, da kuma arzikin man fetir da kasar ke da shi, amma gwamnati ta kasa biyan bukatunsu.

Yace mutane kalilan kadai suke cin moriyar albarkatun kasar, yayinda akasarin al’ummar kasar ke fama da rashi.

Professor Samuel Zalanga ya shawarci gwamnati mai jiran gado kada ta zauna Abuja tana sauraron ‘yan boko, a maimakon haka, ta rika fita tana sauraron koke koken talakawa, ta kuma jajirce wajen ganin masu rike madafun iko sun cika alkawuran da suka yiwa al’umma a lokacin yakin neman zabe.

Ga ci karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hira da Prof. Samuel Zalanga