Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dogaro Da Shawarar Turawa Bai Dace Ba - PDP


Shugaban kasar Najeriya mai jiran gado Muhammadu Buhari, yayi Magana da ‘Yan Jarida Alokacin ziyarar tsohon Faras MInistan Birtaniya Tony Blair A Abuja, Nigeriya, Mayu 13, 2015.

A Najeriya har yanzu ana cece kuce dangane da tafiyar da shugaban kasa mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari ya yi zuwa kasar Burtaniya yayin da ya rage kwanaki kadan a rantsar da gwamnatinsa a karkashin jam'iyyar APC.

Jam’iyyar PDP mai shirin barin mulki a Najeriya, na ci gaba da sukan tafiyar da shugaba mai jirangado, Janar Muhammadu Buhari ya yi zuwa Burtaniya, inda bayanai ke cewa ya je ne domin shirye shiryen kama aiki.

A ranar juma’ar da ta gabata ne, Buhari ya tafi London, babban birnin Burtaniya, a wata tafiya da mukarrabansa suka ce ya je ne ya yi hutun karshen mako tare da shirin karbar mulki.

Sai dai ‘yan jam’iyyar ta PDP suna ta sukan wannan tafiya ganin yadda aka yi ta ba tare da an sanar da ‘yan Najeriya ba.

Bayani dai sun ce Buhari har ya gana da Firai ministan Burtaniya David Cameron a wannan ziyara da ya kai.

"Wannan tafiya da Janar Buhari yayi, zuwa kasar waje ko Turai, abun la'akari Turawannan su suka bamu mulki, kuma sun bar mana mulki, sannan sojoji sun zo, sun kakkarbi mulkin nan, sai muka shiga demokradiyya, to abin lura a nan shine, duk wata niyya ta kowaye, ya koma wajen wadannan turawa a matsayin sune za su iya fada masa abunda zai yi, wannan ba dai-dai bane", a cewar Sanata Walid Jibrin, mukaddashin shugaban kwamitin amitattun na jam’iyar PDP.

Dan majalisar ya kara da cewa "kuma ni ina ganin ganin yadda Buhari ya ke ba zai yi katsalandan na rushe manufofinsa ba a matsayinsa na shugaban da ya ci zabe.”

"Kowane mutum yana da yanayin nazarinsa da yadda zai fara aikinsa, abin lura shi ne ba a gayawa mutane ga abin da ya kai shi ba, wannan shi ne nawa tunanin.” Inji Sanata Jibrin.

A na shi bangaren, mataimakin Kakakin jam’iyyar ta PDP na kasa, Barrister Abdullahi Jalo, ya ce komin dadewa za a ji dalilin zuwan nasa Burtaniya.

“Komai nisan jifa dole zai fado kasa, ma’ana za a ga alherin zuwan nasa ko kuma cikakkun bayanai kana bin da ya kai shi tun da bai fadi koma bayan abin da muka gani a talbijin ba.” Inji Barrister Jalo.

A watan Maris din da ya gabata Buhari ya lashe zaben kasar a karkashin jam’iyyar APC bayan da ya kada abokin hamayyarsa kuma shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan.

Ga karin bayani a hirar da Bello Galadanchi ya yi da Sanata Walid Jibrin da Barrister Abdullahi Jalo:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG