Accessibility links

Abuja: Zabe Ya Daukaka Kimar Najeriya - Abdulsalami

  • Aliyu Imam

Tsohon shugaban kasar Najeriya Abdulsalam Abubakar.

Janar Abubakar yace Najeriya ta zama abar misali a duniya saboda yadda ta gudanar da zabenta cikin lumana.

Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriyan, wanda kuma jigo ne cikin kwamitin tabbatar da zaman lafiya a lokacin da ake gudanar da zabe da bayansa, yace kamin zaben hankalin kowa ya tashi, 'yan arewa dake kudanci da kuma 'yan kudanci da suke arewa kowa ya koma gida, harda baki turawa kowa ya tara komatsansa ya koma gida, domin fargabar "za'a yi tashin kiyama a Najeriya" saboda zabe.

Janar Abdulsalami Abubakar wanda yake magana a hira da yayi da Aliyu Mustapha, yace, akwai bukatar 'yan Najeriya su ci gaba da aiki domin tabbatar da zaman lafiya. Janar mai ritayan yace yanzu kowa ya fahimci muhimmancin zaman lafiya, kuma kowa ya gane cewa muna bukatar juna.

Janar Abdulsalami Abubakar, yace akwai bukatar a jinjinawa shugaba Goodluck Jonathan saboda yadda ya amsa cewa ya fadi zabe, wanda shine karo na farko da shugaba da yake kan mulki ya yarda cewa ya fadi zabe. Al'amari da ya kara karfafa zaman lafiya a cikin kasar.

Tsohon shugaban kasar,yayi magana kan aikace aikacen kwamitinsa na neman zaman lafiya da wasu batutuwa.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG