Zan Bi Sahun Fashola – Inji Akinwumi Ambode

Fasinjoji na shiga motar haya ta bas a Jahar Legas, samar da motocin bas na fasinja na daga cikin ayyukan da Fashola ya yi

Sabon gwamnan jahar Legas, Akinwumi Ambode, ya ce zai ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaban jahar kamar yadda tsohon gwamna Babatunde Raji Fashola ya yi.

Ambode ya bayyana hakan ne a wajen bikin rantsar da gwamnatinsa wacce ta kama aikia ajiya Juma’a.

A jahar ta Legas, babu wata matsala da aka fuskanta kamar yadda aka gani a wasu jahohi, domin Ambode da Fashola duk ‘ya’yan jam'iyyar APC ne.

Ambode ya kuma kara da cewa zai yi aiki da dukkanin al’umar dake jahar ba tare da nuna wariya ba domin ci gaban jahar ta Legas.

“Muddin dai kana zaune ne a jahar Legas, to za mu yi tanadin da za ka ji dadin zaman ka.” Inji Ambode.

Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta kirkiro da wata ma’aikata da za ta kara bunkasa tattalin arziki da kuma samar da aikin yi ga al’umar jahar.

A daya bangaren kuma, a jahar Ogun dake makwabtaka da Legas, an gudanar da rantsuwar inda gwamna Ibikunle Amosun ya yi tazarce wanda shi ma ya yi alkawarin ci gaba da ayyukan da za su kawo daukaka ga jahar.

Ga karin bayani a rahoton wakilin Muryar Amurka a Legas Babangida Jibrin:

Your browser doesn’t support HTML5

Zan Bi Sahun Fashola – Inji Akinwumi Ambode – 2’16”