Wasu yara mata guda biyu - wadanda kafafen yada labarai yankin suka ce ‘yan shekaru hudu da daya ne sun bace bayan da ruwan ambaliyar ya dauke su daga ranar Juma’a.
Ambaliyar ta mamaye dakunan asibitoci, inda ta mayar da unguwanni tamkar tsibirai tare da yanke wutar lantarki a wasu yankunan birnin. Ministar tsaron kasar Patricia Bullrich ta ce ruwan ya lalata Bahia Blanca.
Ya zuwa jiya Asabar, adadin mutanen da suka mutu ya kai 13 daga mutum 10 a ranar Juma’a da hukumomi suka sanar.
Ofishin magajin garin ya ce akwai yuwuwar samun karin asarar rayuka a wannan birni mai al’umma 350,000, mai tazarar kilomita 600 (meli 370) kudu maso yamma da Buenos Aires babban birnin kasar.
Bullrich ta shaidawa gidan rediyon Mitre cewa yaran matan da suka bace "zai iya yiwuwa ruwa ya tafi da su."
Akalla biyar daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su watakila sun makale ne a cikin motocinsu ta hanyar ruwa mai karuwa cikin gaggawa.
Guguwar ta tilasta kwashe mutane daga asibitin Jose Penna, inda labarai da faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta ke nuna ma'aikatan jinya da sauran ma'aikatan lafiya dauke da jarirai zuwa wani wuri mai aminci. Daga baya sojoji ne suka taimaka musu.
Dandalin Mu Tattauna