Hukumomin a Najeriya na bayyana damuwa kan karuwa da ake ci gaba da samu a adadin masu kamuwa da cutar korona birus a kasar inda cibiyar kula da cututtuka masu saurin yaduwa ta NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutane dubu 1 da 56 da suka kamu da cutar a ranar talata kadai.
Ministar ayyukan jinkai ta Najeriya ta ce shirin kadamar da horon sa ido na zamantakewa zai taimakawa 'yan Najeriya kusan miliyan 13 a jihohi da dama.
Hukumar hukumar bunkasa fasahar zamani ta Najeriya NITDA, da hadin gwiwar ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin fasahar zamani, ta kaddamar da aikin gina cibiyar kere-keren fasahohin zamani da kasuwanci.
‘Yan kasuwa na kokawa kan rufe kasuwar Wuse, Abuja sakamakon yadda wasu ’yan kasuwa suka ki mutunta ka’idojin kare kai daga Coronavirus.
‘Yan Najeriya na bayyana ra’ayoyin su game da yiyuwar gwamnatin kasar ta dawo da tallafin man fetur sakamakon tashi a farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Majalisar Dokokin Najeriya ta ce dole hafsosin tsaron kasar su sauka, saboda gazawarsu wajen samar da tsaro.
Tun bayan zanga zangar EndSARS batun makomar dunkulewar Najeriya a matsayin kasa daya al'umma daya ya sake zama wani abin takaddama. Yayin da wasu ke ganin kamata ya yi a raba, wasu na ganin rigimar rabawar ta ma fi matsalar zama tare muni.
Wasu yan Najeriya sun daura alhakin karancin man fetur da zanga-zangar gama gari ta nema kawo karshen ‘yan sandan yaki da ‘yan fashi #EndSARS a kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi jawabi don kwantar da hankulan ‘yan kasa kan kisan matasa masu zanga-zanga.