Zamantakewar Jama'a
Kamar yadda wasu da dama su ka nuna fargaba, an kasa cimma jituwa a tattaunawar da aka yi tsakanin Shugaban Sudan Ta Kudu da jagoran 'yan tawaye, Riek Machar.
Barazanar yaki a fagen cinayyar duniya na dada karuwa yayin da kasar Amurka da tarayyar Turai ke ta gasar maka ma juna haraji.
Yayin da ake ta takaddama kan shigowar bakin haure Amurka ba bisa ka'ida ba, Rundunar sojin Amurka ta yi tayin taimakawa da gina wasu manyan wuraren tsare dubban bakin haure.
Bayan dan tsami da dangantakar kasashen Habasha da Somaliya ta yi, Shugabannin kasashen na yanzu sun sha alwashin karfafa cudanyar kasashen biyu.
Yayin da almundahana ke barazana ga kasar Kenya, Shugaba Uhuru Kenyatta ya yi kukan kura zai dira kan barayin gwamnatin.
Duk da yawan mace-mace da ke faruwa a yayin yinkurin zuwa Nahiyar Turai ta barauniyar hanya, har yanzu ba a daddara ba. Mutane na cigaba da yinkurin zuwa Turai ta kasa da ruwa da kuma sama. A baya-bayan nan an ceto 930 an kuma tsinci gawarwaki hudu a tekun Bahar Rum.
Musulmi a fadin duniya na cigaba da shagulgulan Karamar Salla, wadda aka yi bayan kammala azumin watan Ramadan a ranar daya ga watan 10 wato Shawwal.
Yayin da ake harmar fara wani zagaye na tattaunawa tsakanin bangarorin da ke fada a Afirka Ta Kudu, sai gashi gwamnatin kasar na cewa sai dai a canza kasar da za a yi tattaunawa ta gaba.
Zamantakewar Ja,a'a
A yinkurinsu na maganin gaba, wasu masu ruwa da tsaki sun dau matakin ganin Rasha da sauran kasashe masu salo irin nata ba su yi shishshigi a zaben kasashen yammacin duniya ba.
Kungiyoyin Musulmi da na Kirista sun yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a wasu Majami'u a kasar Indonesiya.
Yayin da Amurka ke shirin bude sabon Ofishin Jakadancinta a Birnin Kudus, ana zaman dardar a yankin Gabas Ta Tsakiya saboda shagulgula da kuma zanga-zangar da ka biyo baya.
A karon farko tun bayan korar mayakan ISIS daga kasar Iraki 'yan kasar sun kada kuri'ar zaben Majalisar Dokokin kasar
Kamar yadda aka zata zai faru, an fara takun saka tsakanin sabon Firaministan Malesiya da tsohon Firaminista kan zargin almundahana da kuma makomar kasar
Domin Kari