An danganta dawowar matsalar mai a sassan Najeriya da wasu matakan da aka dauka da kuma rashin bayar da hadin kai daga ainihin inda ake sayo man.
A cewar kwararru, wa'adin da Shugaban Najeriya ya ba da sojoji na kawo karshen 'yan Boko Haram ya haifar da da mai ido.
Yayin da Majalisar Dattawan Najeriya ke cigaba da tantance sunayen da aka gabatar ma ta na wadanda ake son nadawa Ministoci, Fadar Shugaban Najeriya ta kara sunaye 16; wato adadin sunayen da za a tantance sun kai 37 kenan yanzu.
Yayin da ake hidimomin zagayowar Ranar Takaita Bala'o'in Duniya, Sakatare-Janar din Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon da sauran kwararru da wadanda abin ya shafa sun tashi haikan wajen kiran a dau matakan da su ka dace don kauce ma bala'o'in.
Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana sunayen da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar ma ta don tantancewa.
A cigaba da kokarin tsugunar da mutanen da Boko Haram ta yi wa illa iri-iri, Jahar Adamawa da Hukumar UNICEF sun sha alwashin maida dinbin yaran da ke sansanonin 'yan gudun hijira makaranta.
Yayin da al'ummomi daban-daban a Najeriya ke ta murnar samun ingantacciyar wutar lantarki, wasu al'ummomin jahar Naija mai samar da wutar lantarki ga kasa, na kokawa kan rashin wutar.
Bayan tsige gwamnan jahar Diffa, inda 'yan bindiga su ka kashe wasu mutane da dan dama, kura na cigaba da tashi saboda da banbancin ra'ayi.
Yau kasashen Kamaru da Cadi na cikin wadanda ke jawabai a Majalisar Dinkin Duniya. Baya ga kasashe, akwai kuma kungiyoyi dabandaban da ke gabatar da jawabai da kuma tattaunawa kan al'amuran iri-iri
Yayin da adadin wadanda su ka mutu a hatsarin Saudiyya ya karu, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci hukumonin da abin ya shafa da su tattara cikakken adadin 'yan Najeriya da abin ya shafa.
Yayin da Majalisar Dattawan Najeriya ke jiran sunayen Ministoci daga Fadar Shugaban kasa, Majalisar ta sake gaurewa da rigimar Shugabaci
Hukumomin da abin ya shafa na cigaba da ba da tabbacin cewa su na daukar matakai daban-daban na ganin an yi bukukuwan Sallah lafiya lau.
Yayin da matasa ke kafa hujja da dalilai dabandaban na shan kayan maye da su ke yi, kwararru sun bayyana illoli masu muni da kayan mayen ke haddasawa
Yayin da Kungiyar Habbaka Tattalin Arzikin Afirka (ECOWAS) ke taro a Abujan Najeriya, wani kwararre ya ce ga dukkan alamu, wannan karon taron kungiyar zai yi nasara saboda sauye-sauyen da ake samu a Nahiyar.
Kotun Tabbatar Da Da'ar Ma'aikata ta ce Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya je gida ba tare da beli ba; ganin ya je kotun da kansa.
A cigaba da kallon hadarin kajen da ake wa juna, Koriya Ta Kudu ta gargadi Koriya Ta Arewa da kar ta kuskura ta gwada harba roka mai dogon zango.
Yayin da ya ke shan suka daga yammacin duniya, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya kare matakin soji da kasar ke daukawa a Siriya
Kwanciyar hankalin da aka samu a Najeriya ya sa har wasu 'yan Janhuriyar Nijar da su ka gudu lokacin da tashin hankalin Boko Haram ya yi tsanani sun fara dawowa
A cigaba da kokarin ganin yankin arewa maso gabas ya farfado, 'yan Majalisar Tarayyar da su ka fito daga yankin sun hada kai wajen ganin cewa an kafa wata doka kwatankwacin ta NNDC.
A wani abin tarihi da aka yi a Jami'ar Jos, an samu nasarar kirkiro wasu muhimman magunguna, ciki har da na cizon sauro da na cizon macizai da dai sauransu.
Domin Kari