Gwamnatin jahar Lagos ta hana sana'a a gefen titi, amma wadanda abin ya shafa na kokawa
An yi asarar dinbin kudi a kasuwar hannayen jarin Najeriya, al'amarin da wasu kwararru ke dangantawa da matakan gyara kasa da gwamnati mai ci ke daukawa
A cibaga da barnar da ambaliyar ruwa ke yi a arewacin Najeriya, wasu unguwanni a Maiduguri sun dandana barnar ambaliyar ruwa, wanda ya janyo kokekoke daga mazauna unguwannin.
Ga dukkan alamu kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) na taronta na karo na 55 a daidai lokacin da ake matukar bukatar gudunmowarta, ganin kasar na kokarin ganin bayan masu cin hanci da rashawa da kan samu daurin gindin wasu ma'abuta shari'a.
Yayin da jahar Taraba ke fuskantar karuwar rigingimun siyasa, sai ga shi kuma ta fada rigimar rashin biya albashi.
Yayin da Najeriya ke ta karbar bakucin muhimman mutane daga sassan Najeriya, kwararru na danganta al'amarin da karbuwar da kasar ke samu
Ga dukkan alamu taron dangi ya fi fa'ida a yakin da ake yi da barayin shanu ganin yadda aka yi ta damke miyagun bayan da jahohi biyar su ka yanke shawarar hada kai.
A yayin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke cigaba da yin fito-na-fito da batun cin hanci da rashawa, ana cigaba da yaba masa. Saidai kuma ana kuma ganin masu dokar barci a hukumomin yaki da cin hancin su ma sun shiga gyangyandi.
Rigimar da akan yi kan batun daukaka wasu kwalejojin Ilimi zuwa jami'o'in koyon aikin malanta ta dau wani sabon salo, bayan da hadakar kungiyoyin malamai da ma'aikatan Jami'o'i shiyyar Jami'ar Koyon Aikin Malanta ta Kano ta yi zargin cewa ana nan ana ta kokarin yin zagon kasa ga sabbin jami'o'in, alhalin kuwa su na iya rayuwa.
Yayin da matakin hana adanar dala a bankin Najeriya ke gamuwa da suka daga wasu 'yan kasa, musamman 'yan adawa, da alamar matakin ya daga darajar Naira.
Zargin bacewar kudi ko rashin bacewarsu ya janyo murza gashin baki tsakanin 'yan jam'iyyar APC da PDP a jahar Naija.
A cigaba da agaza ma wadanda Boko Haram ta cutar, kungiyoyin da ba na gwamnati ba sun kafa hadaka don taimaka ma mabukatan
Bangaranci da sauran rigingimu sun dabaibaye taron matasan Najeriya da aka yi a Abuja
Wasu malamai sun lura cewa rikicin Falasdinu na da nasaba da wariyar jinsi. Don haka sun ce sai an shawo kan wannan matsala ta sauya tunanin mututanen yankin ga tafarkin zama tare kafin a yi nasarar tabbatar da zaman lafiya a yankin.
A cigaba da hada kai da kasashen da Boko Haram ke addaba ke yi, Shugaban Najeriya zai gana da Shugaba Paul Biya na Kamaru don kara inganta shirinsu na yi wa Boko Haram taron dangi
Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ke kokarin farfado da tattalin arzikin kasar, kwararru na fargabar cewa faduwar farashin mai a kasuwannin duniya na iya kawo wani cikas din -- to amma akwai magana -- amma mai daci.
Yayin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke kokarin samun taimakon Amurka wajen yaki da Boko Haram, kungiyar ta kai wani hari a Damaturu, inda ta hallaka mutane 4, na bayabayan nan a jerin hare-haren da kungiyar ke kai wa
Sanadiyyar zuwan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Amurka, an shiga tattaunawa tsakanin Najeriya da Amurka game da tsaro, cinakayya da sauran abubuwa.
Kwararru a Najeriya na cigaba da tsokaci kan sauya manyan jami'an soji da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi don kara azama a yakin da ake yi da Boko Haram
Yayin da 'yan Boko Haram ke kara tayar da kayar baya cikin 'yan kwanakin nan, mutanen garin Damasak sun gudu saboda sojojin Chadi masu kare su sun janye.
Domin Kari