Yau Laraba shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, ya ayyana gwamnar Jahar North Carolina, Nikki Haley a matsayin Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya. Kuma itace mace ta farko da ya nada a majalisar zartaswarsa.
Daliban jami'o'i a Kenya, abubuwan da suke koya sun wuce maganar karatu da lokutan Jarrabawa ko kuma Karatun dare, Wasu shugabannin a Jami’o'i a sun yi zaman ganawa a Nairobi a wannan mako domin tattauna akan batututwa da suka shafi daliban , ciki har da Tashe tashen hankula, Manyan Laifuffuka da kuma wankin-kai da kuma Tsatstsauran ra’ayi.
Kotun soja a garin Maiduguri ta yanke hukunci ga wasu jami’an soja guda hudu kan wasu laifuffuka da suka aikata daban daban a lokacin da suke gudanar da yaki da mayakan kungiyar Boko Haram.
Kwararru a fannin ilimi a Najeriya na ci gaba da yin sharhi dangane da ikirarin da hukumar shirya jarabawar shiga Jami’o’i ta Najeriya JAMB tayi cewa kashi 80 na daliban dake zana jarabawar neman shiga Jami’a basu da cancanta.
Kungiyoyin addinan Krista da Musulunci a Najeriya sun dukufa wajen fadakar da al’umma illar cin hanci da rashawa a tsakanin jama’a.
An jihar Lagos an bude wani taron yini biyu akan hanyoyin samar da wutar lantarki a Najeriya.
MDD ta bada rahoton cewa ana cigaba da samun Karin ‘yan Iraki masu gudun hijira sakamakon farmakin da sojoji ke kaiwa don sake kwato birnin Mosul dake Arewacin kasar daga hannun ‘yan ISIS.
Shugaban Amurka mai jiran gado ya ce ranar farko da zai fara aiki cikin abin da zai yi har da fidda sanarwar a hukumance cewa Amurka ta janye daga yarjejeniyar cinikayya da ake kira Trans-Pacific, ko TPP a takaice, abin da ke cikin jerin kudurorinsa akan sanya muradan Amurka kan gaba.
A cikin tsanaki da taka tsan-tsan kasar kamaru ta bude iyakarta da Najeriya, inda ta fara gudanar da kasuwanci, shekaru 3 bayan da ta rufe iyakar sakamakon rikicin ‘yan Boko Haram.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, ICPC, ta gudanar da taron wayar da kan jama’a kan matakan hana cin hanci da rashawa a tsakanin al’umma musamman a ma’aikatun gwamnati da kamfanoni da ma’aikatu masu zaman kansu.
Masana harkokin tattalin arziki na ci gaba da fashin baki dangane da hauwahawar farashin takardun kudi na Dala a Najeriya, duk kuwa da kamen da Jami’an tsaro na kasar ke yiwa ‘yan canji a kasuwannin musayar kudade a birnanen Kano da Abuja da kuma Lagos.
An bada belin wani babban Jojin kotun koli Sylvester Ngwuta da aka gurfanar a gaban wata kotun Tarayya a Abuja akan kudi Naira Miliyan 100, bayan da aka zargi Jojin da aikata laifuka 15.
Kasar Mali ta gudanar da zaben kananan hukumomi da aka dade ana jinkirtawa.
Kungiyar nan mai kare hakkin bil adama ta Huma Rights Watch, ta ce ta na da hujja da ta samu ta tauraron dan adam, dake nuna cewa an rusa fiye da gidaje dubu daya mallakar ‘yan kabilar Rohingya a Arewa maso yammacin Myanmar ko kuma kasar Burma.
Jami’ai a Afghanistan sunce Bam din da dan kunar bakin wake ya tayar a Masallacin Yan Shi’a a Kabul a Yau Litinin ya kashe sama da mutane 30 ya kuma jikkata wasu 85.
Bincike ya nuna cewa an samu ci gaba ta sosai ta bangaren harkar noma a wasu jihohin Najeriya, shekara da shugaban kasa Mohammadu Buhari ya kaddamar da shirin noman Shinkafa da Alkama da kuma bada tallafin bashi ga manoma ta hannun babban bankin Najeriya a jihar Kebbi.
Gwamnan babban bankin Najeriya ya baiwa gwamnati shawarar duba yiwuwar fara karbar haraji daga masu buga wayar salula da ya haura mintuna uku, domin samun kudin shiga.
Ministan matasa da wasannin Najeriya Solomon Dalung, ya musunta rahotannin da kafofin yada labarai suka fitar cewa Najeriya na shirin ficewa daga gasar cin kofin duniya da za a gudanar a kasar Rasha.
Noma Tushen Arziki
Majalisar Dattawan Najeriya zata hada gwiwa da Majalisar Wakilai domin a kafa hukumar da za ta rage radaddin talauci a kasar.
Domin Kari