Amurka ta yi watsi da ikirarin Rasha cewa, gubar iskar nan da ta yi sanadin mace-mace mai yawa a Siriya makon jiya, ta fashe ne a ma'adanar makaman 'yan tawayen Siriya inda aka boye ta, bayan da aka kai harin jirgin sama. Wani rahoton Amurka ya nuna cewa lashakka wannan gubar iska da niyya aka bada ta kan farar hula.
A baya bayan nan karo na hudu kenan hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC, na shan kaye a gaban Kuliya dangane da yunkurin da ta ke yi na kwato wasu makudan kudade daga hannun wasu mutanen da ta zarga da yin sama da fadi.
A kasar Sudan ta Kudu, Shedun gani da ido sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga cikin kayan soja a garin Wau jiya littini sun kashe mutane da dama kana wasu da dama sun samu rauni.
Sojojin Amurka da na Afghanistan dake gabashin kasar ta Afghanistan sun samu nasarar kakkabe ‘yan kungiyar ISIS daga wasu muhimmam wuraren da kungiyar take rike dasu tun a shekarar 2015.
Sojojin Amurka sunce suna nan suna iya bakin kokarin su, na ganin sun kara samar da hanyar da zata rage yiyuwar fito na fito da kasar Rasha akan maganar Syria.
Rundunar sojan Najeriya ta Operation Lafiya Dole dake garin Maiduguri ta mika wasu mutane da ta wanke su 593 da aka kame lokaci da ake yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram ga gwamnatin jihar Borno.
A wani yunkuri na tallafawa yara yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya shafa, rundunar sojin Najeriya ta kai tallafin kayayyakin karatu da na rubutu ga dubban yara dake sansanonin yan gudun hijira dake jihohin Adamawa da Taraba.
Sabon Hafsan sojin Somaliya, Janar Ahmed Muhammed Jimale Irfid, ya tsallake rijiya da baya a wani harin kunar bakin waken da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 15 kusa da tawagarsa a Mogadishu, a cewar jami'an gwamnati.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci shawarar jami'ai, kan yadda zai kawo karshen barazanar nukiliya daga Koriya Ta Arewa. Mai ba Kasa Shawara kan Tsaro Herbert Raymond McMaster ne ya fada jiya Lahadi.
Kungiyar ISIS ta yi ikirarin ita ta kai hare-hare a wasu majami'u biyu na Kubdawan Masar, da su ka yi sanadin mutuwar mutane 44 da kuma raunata sama da 100 yayin da ake ibadojin Ista.
Jakadiyar Amurka a MDD ta bayyana cewa Shugaban Amurka Donald Trump na iya sake kai hari Siriya muddun bukatar hakan ta taso.
Hedikwatar ‘yan sandan Najeriya ta maida martani bisa zargin da gwamnan jihar Rivers ya yi cewa Sufeto janar na ‘yan Sanda ya baiwa kwamishinan ‘yan Sandan jihar umarnin ya halaka shi.
Rahotanni daga jihohin Adamawa da Taraba dake Arewa maso Gabashin Najeriya na nuni da cewa yanzu haka ana fama da matsanancin zafi, lamarin dake kara matsalar cutar sankarau da yanzu haka ta hallaka jama’a da dama a kasar.
Noma Tushen Arziki
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya fara ran gadin sa a kasashen Asiya zagaye na biyu, inda yau Juma'a ya sauka Koriya ta Kudu
Mutane 42 ne suka mutu kana wasu da dama suka samu rauni, sakamakon harin da aka kaiwa ‘yan tawaye a wani masallacin da yan tawayen ke rike dashi a arewacin Syria, kamar yadda kungiyar nan da ake kira da turaci Syrian Observatory for Human right ke cewa.
Wasu mayakan Boko Haram guda tara sun ajiye makamansu sun kuma mika wuya ga sojojin Najeriya a ‘kauyen Tambashe dake karamar hukumar Dikwa ta jihar Borno.
Jam’iyyar adawa ta Najeriya PDP ta shigar da ‘kara babbar kotun tarayya ta na bukatar a kori Sanata Nelson Effiong, daga Akwa Ibom don ficewa daga jam’iyyar zuwa APC mai mulki.
Masana harkokin shari’a da dokokin kasa na ci gaba da bayyana ra’ayi dangane da kin tabbatar da Ibrahim Magu ya zama shugaban hukumar EFCC da kuma takaddamar da ke wakana tsakanin Majalisar da shugaban hukumar kwastam ta kasar Kanal Hamid Ali mai ritaya.
A Netherlands sakamakon farko na zaben kasar da aka yi jiya Laraba, ya nuna jam'iyyar Fara Ministan kasar Mark Rutte's, ta lashe kujeru mafi yawa a majalisar dokokin kasar, ta doke jam'iyyar dake adawa da baki da kuma addinin Islama ta dan kishin kasa Geert Wilders, da rata mai yawa wadda ba'a yi zaton tazarar ta kai haka ba.
Domin Kari