Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Fararen Hula A Sudan Ta Kudu


Sudan ta Kudu
Sudan ta Kudu

A kasar Sudan ta Kudu, Shedun gani da ido sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga cikin kayan soja a garin Wau jiya littini sun kashe mutane da dama kana wasu da dama sun samu rauni.

Wadannan mutanen da suka yi kama da sojojin gwamnati sun bi gida-gida suna kashe farar hula kana suna kwashe kayan su.

Odoongi Simon wani mazaunin garin Wau dake makwabtaka da Nazareth yace, wannan lamarin ya fara ne da jin karar bindiga a yankin na Nazereth inda wuri ne dake da ‘yan kabilar Luo da Fertit a garin na Wau.

Yace sunga yadda ake ta jawo mutane daga cikin dakunan su, kuma da zaran an gane ‘yan kabilar Luo ne ko na Fertit nan take sai a kashe su.

Simon yace mutanen masu aikata wannan danyen aikin cikin kayan soja, da wasu cikin farin kaya, sune suke bi gida-gida tun da safiyar jiya littini, suna fito da yan wadannan kabilun wadanda farar hula ne suna musu kissa, kana suna kwashe kayan su, daga bisani kuma su kona gidajen su.

Yace wannan lamari yasa harkokin kasuwanci, makarantu da wasu ofisoshin gwamnati duk an kulle su.

Yace al’ummar wannan gari suna zaune ne cikin zaman tashin hankali,dominko ba mai fitowa daga dakin sa musammam wadanda suka san cewa ana farautar su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG