Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Sauka a Koriya Ta Kudu


Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya fara ran gadin sa a kasashen Asiya zagaye na biyu, inda yau Juma'a ya sauka Koriya ta Kudu

A sa’ilin wannan ziyarar dai Tillerson zai gana da manyan jamia'an koriyan ta Kudu da kuma wurin da ya raba Koriyoyin biyu.

A zagayen ran gadin nasa na farko Tillerson ya fada jiya alhamis a Tokyo cewa akwai bukatar bude wani sabon babi na hana Koriya ta Arewa samar da makamin nukiliya, wanda aka gaza yi a cikin shekaru 20.

Tillerson yace daya daga cikin manya-manyan dalilan sa na wannan ran gadin, shine musayar ra’ayi tsakanin sa da Japan,Koriya ta kudu da kuma China akan hanyar da za a samu ci gaba.

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa da sakataren harkokin wajen Amurkan yayi da takwaran sa na kasar Japan Fumio Kishida, yace kar wani abu yaba Koriya ta Arewa tsoro gamne da Amurka, don haka yana kira ga Koriya ta Arewa data jingine batun ta na samar da makamin Nukiliya da kuma duk wani abu daka iya kawo tada jijiyan wuya.

Sai dai kuma ya jaddada manufar Amurka na kare Japan da kuma sauran kawayen Amurka.

Zagayen ziyarar tasa ta karshe ita ce kasar China inda zai gana da shugaba Xi Jimping.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG