No media source currently available
Masarawa sun yi sallar Juma'a jiya a cikin masallatai bayan an dakatar da hidimomin na tsawon watanni saboda annobar Coronavirus. An fara yin ibada a masallatai ne bayan an sami raguwar adadin cutar a cikin kasar a watan Agusta. "Duk muna farin ciki, yau kamar hutu" in ji wani da ya je yin salla.
A Switzerland Hukumar lafiya ta duniya ta sanar da karuwar sabbin kamuwa da coronavirus cikin rana guda a fadin duniya da ya kai mutum dubu 230, 370. Kasashen Amurka da Brazil da India da Afrika ta Kudu ne suka sanar da karuwa mafi yawa.
A Australiya, Jihar Victoria ta bada rahoton sabbin alkaluman kamuwar cutar coronavirus 288 a wuni daya yau Jumma’a. An gudanar da gwajin cutar da dama da ya zarta dubu talatin da bakwai da dari biyar.
A Australiya Jami'an birnin Melbourne sun ce an gano sabbin masu dauke da coronavirus guda 191, inda suka ba da umarnin sake dakatar da harkoki har tsawon makwanni 6.
Kasar India ta zarta kasar Rasha wajen zama kasa ta 3 da fi yawan masu cutar coronavirus bayan da ta samu mutun dubu 24,000 sabbin kamuwa a yau litinin. Yanzu India na da masu corona kusan dubu 700,000.
Dr. Anthony Fauci, darektan daraktan cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta Amurka kan muhimmancin amfani da takunkumin rufe fuska, da kuma kokarin da ake yi na samar da rigakafi