Kwanan nan Shugaba Buhari ya gana da shugaban Amurka Donald Trump a birnin Washington DC. Me za ku ce akan batutuwa 10 da suka bayyana wanda Sashen Hausa na Muryar Amurka ya gano.
A lokacin da Shugaba Buhari ya kawo ziyara Amurka, tawagarsa ta gana da kusoshin shahararren kamfanin kera jiragen sama na Amurka, wato Boeing kan batun sake kafa kamfanin sufurin sama na kasa.
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya ce bai gamsu da cewa matakin barin jihohi su kafa rundunar ‘yan sandansu shi ne zai kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar.
A wata doguwar fira da ya yi da babban editan Sashen Hausa shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bayyana cewa shugaban Amurka ne ya gayyaceshi kana ya tabo batutuwan da suka tattauna tare, har da zargin cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya
Sakamakon ziyarar shugaban Najeriya Buhari zuwa fadar shugaban Amurka Donald Trump, shugaban na Amurka wanda a baya ya sha suka bisa ga kalamun batanci da ya yi akan kasashen Afirka amma sai gashi a wannan lokacin ya nuna sha'awar kai ziyara Afirka
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da na Amurka Donald Trump a taron manema labarai a fadar White House da ke birnin Washington, D,C.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugaban Amurka Donald Trump yau Litinin a birnin Washington DC, wannan ne karon farko da wani shugaba daga nahiyar Afrika ya kai ziyara fadar White House a wannan shekarar ta 2018.
'Yan yankin kudu maso gabashin Najeriya mazauna Amurka, wadanda ke son a raba Najeriya su koma Biafra, na zanga zanga a wajen fadar shugaban Amurka da kan zuwan shugabn Najeria Muhamadu Buhari birnin Washington DC.
Domin Kari