Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban Gamsu Da Kafa ‘Yan Sandan Jihohi Ba - Buhari


'Yan Sanda Suna Faretin Suna Ban Girma a Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Najeriya, Muhammad Buhari

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya ce bai gamsu da cewa matakin barin jihohi su kafa rundunar ‘yan sandansu shi ne zai kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar.

Buhari ya yi wannan magana ce a lokacin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka, bayan ganawarsa da shugaba Trump.

A cewar Buhari yanzu wasu jihohin Najeriya ba sa iya biyan albashin ma’aikatansu, balle kuma a ce za su iya daukan nauyin rundunar ‘yan sandansu.

Shugaban dai ya ce a yanzu hankalinsa bai kwanta ba akan barin jihohi su mallaki ‘yan sandan kansu ba, amma sai an duba tsarin mulki domin tabbatar da abin da doka ta tsara kafin a san abin da za ayi.

Haka kuma shugaba Buhari ya amince da daukar ma'aikatan 'yan sanda 6,000 a matsayin wani ɓangare na matakan da za su magance matsalolin tsaro na kasa da suka hada da manoma da makiyaya a fadin kasar.

Domin karin bayani saurari kadan daga cikin hirar da aka yi da shugaba Buhari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG