Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansanda A Afirka Ta Kudu Sun Kashe Masu Zanga-Zanga Kusan 20


'Yansanda a Afirka ta kudu suka bude
‘Yansanda sun fesa ruwa da hayaki masu sa hawaye kan gungun masu zanga-zangar, sannan daga bisani suka bude musu wuta, a harabar kamfanin hakar ma’adinai da ake kira Lonmin PLC.

Kamfanin yana arewa maso yammacin birnin Johanesburg da tazarar kilomita 120.
'Yansanda suke bude wuta kan ma'aikata dake yajin aiki a wani kamfanin tama da karafa.
'Yansanda suke bude wuta kan ma'aikata dake yajin aiki a wani kamfanin tama da karafa.

Wani kakakin kungiyar ma’aikatan hakar ma’adinai ya gayawa MA cewa jami’an kungiyar sun hakikance cewa an kashe mutane akalla 12 zuwa ashirin.

Kamfanin dillancin labarai na kasar SAPA yace wakilinsa ya kirga gawarwaki 18.

Wani kakakin kungiyar Lesiba Seshoka, yace akwai alamun ma’aikatan dake yajin aiki su suka fara kai hari.
XS
SM
MD
LG