Accessibility links

An Harbi Shugaba Mohammed Ould Abdelaziz Na Mauritaniya


Shugaba Mohammed Ould Abdel Aziz na Mauritaniya (dama) a lokacin da ya je tarbar gawarwakin malaman kasar da aka kashe a Mali.
Jami'ai a kasar Mauritaniya sun ce yau lahadi za a dauki shugaba Mohammed Ould Abdel Aziz zuwa wata kasar waje domin yi masa jinyar raunin da ya samu a bayan da aka harbe shi ranar asabar a wani abinda jami'an gwamnati suka ce kuskure ne.

An harbi shugaban lokacin da yake tafiya cikin wata kwambar motoci a kusa da Nouakchott, babban birnin kasar, jiya asabar. Jami'ai suka ce harbin an yi shi ne bisa kuskure a bayan da wasu jami'an tsaro dake sintiri a kan hanyar da yake shigewa suka kasa gane cewar kwambar motocin shugaban ne.

Amma wasu rahotanni daga kasar sun ce wata kungiyar 'yan tsagera ce ta lkai hari kan shugaban a kan hanyarsa ta zuwa garin Tweila dake arewa da babban birnin kasar, inda ya saba zuwa kusan kowane karshen mako domin hutawsa.

Wasu rahotanni sun ce za a kai shi jinyar ce a kasar Faransa.
XS
SM
MD
LG