Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Akalla 20 A Kofar Wani Masallaci


Sojoji a hanya su na binciken ababen hawa a Kawo, Kaduna.
Jami'an gwamnatin Najeriya sun ce wasu mutanen da ake kyautata zaton 'yan fashi ne, sun bude wuta a kofar wani masallaci a arewacin kasar, suka kashe mutane akalla 20.

Hukumomi suka ce an kai harin ne yau lahadi da asuba a kauyen Dogon Dawa dake Jihar Kaduna.

Wani jami'in aikin ceto a jihar wanda ke zaune kusa da inda wannan abu ya faru, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa 'yan bindiga kimanin hamsin ne suka kewaye kauyen da gonakin mutanen kauyen. Wasu daga cikin wadanda aka kashe, su na fitowa ne daga Masallaci bayan sallar asubahi.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin, amma jami'ai sun ce sun yi imani 'yan fashi ne suka kai hari domin ramuwar gayyar wasu 'yan'uwansu da suka mutu a hannun 'yan banga na wannan yanki.

Dubi ra’ayoyi (2)

An rufe wannan dandalin

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG