Accessibility links

Mutanen da ba a san adadinsu ba sun mutu lokacin da 'yan bindiga suka kai hari kan wani sansanin soja a kusa da Bissau, babban birnin kasar yau lahadi

Musayar wuta da bindigogi a kasar Guinea-Bissau yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 6, yayin da kasar dake fama da fitina take kokarin farfadowa daga juyin mulkin soja da ya wargaza zaben shugaban kasa a wannan shekarar.

Majiyoyi sun fadawa kamfanonin dillancin labarai na kasashen yammaci cewa an fara musanyar wutar a lokacin da wasu ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba suka kai hari da asubahin yau lahadi a kan wani sansanin soja dake kusa da Bissau babban birnin kasar. Sojoji sun mayar da wuta suka fatattaki maharan. Majiyoyin sun ce da alamun akasarin wadanda aka kashe maharan ne. Har yanzu ba a san irin hasarar rai ko raunin da dakarun tsaro suka samu a wannan fada ba.

Sojoji sun kwace mulki cikin watan Afrilu a kasar Guinea-Bissau a yayin da ake shirin gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa. Shugabannin juyin mulkin sun nada gwamnatin rikon kwarya a watan Mayu domin ta shirya sabon zabe, matakin da ya samu goyon bayan kungiyar Tarayyar tattalin Afirka ta Yamma, ECOWAS.

Kasar Guinea-Bissau ta yi ta fama da fitinu tun lokacin da ta samu ‘yancin kai daga kasar Portugal a shekarar 1974, inda ta yi ta ganin juye-juyen mulki. Wannan rashin kwanciyar hankali ya sa kasar ta zamo cibiyar yada zango na masu safarar hodar iblis ta Cocaine.
XS
SM
MD
LG