Accessibility links

Kwamitin Rantsar Da Shugaba John Dramani Mahama Zai Yi Zama Yau Jumma'a


Magoya bayan shugaba John Dramani Mahama na Ghana su na murna a titunan Accra, bayan da aka ce shi ya lashe zabe.

Kwamitin yace zai yi zaman farko yau jumma'a, duk da cewa jam'iyyar hamayya ta NPP ta shiga kotu tana kalubalantar sakamakon zaben

Kwamitin shirya bukin rantsar da shugaba John Dramani Mahama na kasar Ghana yana ci gaba da shirinsa na ganawar farko yau jumma’a, duk da cewa babbar jam’iyyar hamayya ta kasar ta kalubalanci sakamakon zaben da ya ba shugaban nasara.

Ayyukan da wannan kwamiti zai gudanar sun hada har da aza harsashin bukukuwan rantsar da shugaba da za a yi ranar 7 ga watan Janairu.

A cikin hirar da yayi da Muryar Amurka, wani wakili a kwamitin shirya bukin rantsar da shugaban, Agyeman Badu Akosa, yace kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotu ba zai shafi ayyukan da wannan kwamiti zai gudanar ba. Yace zasu ci gaba da ayyukansu har sai lokacin da kotu ta zartas da hukumci a kan ko za a rantsar da shugaban ne ko a’a.

Jam’iyyar hamayya ta NPP ta kalubalanci sakamakon zaben, tana mai cewa tana da isasshiyar shaidar da zata sa ta je gaban kotu neman hakkinta.

Hukumar zabe ta Ghana ta ce shugaba Mahama shi ya lashe zaben da kimanin kashi hamsin da rabi daga cikin 100, yayin da Nana Akufo-Addo na jam’iyyar NPP yazo na biyu da kimanin kashi 48 daga cikin 100.

Wannan sakamako yasa shugaba Mahama zai fara yin cikakken wa’adinsa na farko kan mulki. A yanzu dai yana kammala wa’adin shugaba John Evans Atta-Mills ne wanda ya rasu kan wannan kujera.
XS
SM
MD
LG