Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

John Dramani Mahama Ya Lashe Zaben Shugaba A Ghana


'Yan Jam'iyyar NDC su na murnar nasarar da dan takararsu, John Dramani Mahama, ya samu a zaben shugaban kasa, 9 Disamba 2012

Hukumar zabe ta ayyana nasarar Mahama yayin da 'yan jam'iyyar hamayya ta NPP suka bazu kan titunan Accra, su na zargin an yi magudi.

Shugaba John Dramani Mahama na kasar Ghana ya lashe zaben shugaban kasar Ghana, ya doke Nana Akufo-Addo na jam'iyyar hamayya ta New Patriotic Party, ko NPP a takaice.

Da maraicen lahadin nan hukumar zabe ta kasar Ghana ta fito ta ayyana cikakken sakamakon, jim kadan a bayan da ta wallafa shi a dandalin Facebook. Wannan sanarwa ta biyo bayan zaman dar-dar da aka yini ciki, tare da zarge-zargen magudi da kuma zanga-zanga.

Tun da fari, daruruwan magoya bayan jam'iyyar hamayya sun bazu kan titunan birnin Accra, babban birnin kasar, a bayan da jam'iyyarsu ta NPP ta yi zargin cewa an tabka magudi, ta kuma bukaci da a sake tantance sakamakon kafin a bayyana shi.

A lokacin da zanga-zangar ta yi tsanani ma, Kwamishinar 'yan sanda ta kasar Ghana, Rose Bio-Atinga, ta nemi kwantar da hankulan al'ummar kasar, tana mai fadin cewa jami'ansu su na ko ina, dare da rana, kuma za su tabbatar da kare lafiyar jama'a.

Kasar ta Ghana dake Afirka ta Yamma ta yi suna a zaman mai kwanciyar hankali a wannan yanki dake fuskantar tashe-tashen hankula dabam-dabam, a saboda yadda take gudanar da zabubbukan dimokuradiyya tare da mika mulki cikin lumana.

'Yan kallo na kasar da kasa sun ce da alamun an gudanar da zaben ba tare da ha'inci ba, duk da cewa an ci gaba da jefa kuri'a har zuwa asabar a saboda matsalar kayan aiki da ta na'ura da aka samu ranar jumma'a.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG