Accessibility links

Buzaye Sun Kama Manyan Jami'an 'Yan Kishin Islama


Kwambar sojojin Mali kusa da Hambori, dake kan hanyar Gao a arewacin Mali, ranar Litinin 4 Fabrairu 2013.

Kungiyar ‘yan awaren Buzaye ta MNLA ta ce ta kama Mohammed Moussa Ag Mohammed da Oumeini Ould Baba Akhmed a kusa da bakin iyaka da Aljeriya.

An kama manyan jami’an kungiyoyin kishin Islama guda biyu a yankin arewacin Mali, cikinsu har da wani babban shugaba na kungiyar Ansar Dine.

Kungiyar ‘yan awaren Abzinawa ko Buzaye ta MNLA ta ce ta kama Mohammed Moussa Ag Mohammed da Oumeini Ould Baba Akhmed ranar asabar a kusa da bakin iyakar Mali da Aljeriya.

Ag Mohammed shi ne na uku a girma cikin kungiyar Ansar Dine, kuma ya taimaka wajen kafa tsarin fassarar shari’a mai tsauri a birnin Timbuktu.

An yi imanin cewa Baba Akhmed dan kungiyar nan ce ta Hadin Kai da Jihadi a Afirka ta Yamma, wadda aka fi sani da sunan MUJAO a takaice.

Kungiyoyin biyu tare da Kungiyar al-Qa’ida ta yankin Maghreb sun mamaye manyan garuruwan dake arewacin Mali na tsawon watanni 9 kafin sojojin Faransa da na Mali su fatattake su.

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, ya fada jiya litinin cewa har yanzu jiragen saman yaki na Faransa su na ci gaba da kai farmaki a kan hanyoyin jigilar kaya da sansanonin horaswa dake can lungu cikin hamadar yankin arewa maso gabashin Mali. Ya fadawa gidan rediyon Faransa cewa makasudin hakan shi ne tabbatar da cewa ‘yan tawayen ba su samu sukunin iya zama na lokaci mai tsawo a yankin arewacin Mali ba.

A jiya litinin din kuma, mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden, ya gana da shugaba Francoise Hollande na Faransa a Paris, inda ya yaba da farmakin da Faransa ta kai a Mali, yana mai bayyana shi a zaman wanda yayi nasara fitacciya.
XS
SM
MD
LG