Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirgegen Dutse Daga Samaniya Zai Gitta Ta Kusa Da Duniya


Wanui curin Dutse mai suna Apophis dake yawo cikin sararin subhana. Irinsa zai kusanto duniya ranar Jumma'a 15 Fabrairu 2013

Wannan dutse mai fadin mita 45 ko rabin filin kwallo, zai kusanci dunkiya fiye da wasu taurarin dan Adam na sadarwa a ran Jumma'a mai zuwa

Hukumar Binciken sararin Samaniya ta Amurka, NASA, ta ce a mako mai zuwa, wani shirgegen dutse daga sararin subhana zai gitta ta kusa da kusa sosai da duniya, amma kuma babu wani abin tsoro, ba sai mutane sun sheka sun nemi mafaka cikin kogo ko ramukan karkashin kasa ba.

Wannan dutse zai wuce kimanin kilomita dubu 27 da 520 daga kan doron kasa ta bisan tekun Indiya da misalin karfe 7 da minti 24 na yamma agogon UTC, watau karfe 8:24pm agogon Najeriya, ranar jumma’a mai zuwa 15 ga watan Fabrairu. Masana kimiyyar samaniya na hukumar NASA wadanda suka auna falakin da wannan dutse mai fadin mita 45, ko rabin filin kwallon kafa ke bi, sun ce babu ta yadda zai ci karo da duniya.

Wannan dutse da zai gilma da sauri ba za a iya ganinsa da kwayar ido ba saboda ba ya da girma kuma yana da nisa daga doron kasa, amma masu tabaron hangen nesa zasu iya ganinsa kamar tauraro yana shigewa da sauri kusa da duniya fiye ma da wasu taurarin dan Adam na sadarwa.

Hukumar NASA ta ce wannan dutse na daya daga cikin mafiya girma da suka zo kusa sosai da duniyar bil Adama, amma shekaru aru aru da suka shige, wadanda suka fi shi girma ma sun sha fadowa kan duniya su na hallaka halitta da barna maras misaltuwa.

Irin wannan dutse na baya da yayi mummunar barna shi ne wanda ya fado kan dajin Tunguska a Siberia ta kasar Rasha a shekarar 1908, ya kwantar da bishiyoyi na tsawon daruruwan kilomitoci a kewayen inda ya abka.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG