Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Hafsoshin Sojan Guinea Sun Mutu A Liberiya


\Masu aikin ceto a inda jirgin saman manyan hafsoshin sojan Guinea ya fadi a kusa da Monrovia babban birnin Liberiya, Litinin 11 Fabrairu, 2013.

Babban hafsan sojojin Guinea, Janar Souleymane Diallow, tare da manyan hafsoshin kasar da dama sun mutu lokacin da jirginsu ya fadi kusa da Monrovia, babban birnin Liberiya.

Babban hafsan sojojin kasar Guinea da wasu manyan hafsoshin sojan kasar sun mutu a cikin wani jirgin saman da ya fadi a kasar Liberiya.

Jami'ai a kasashen Guinea da Liberiya sun ce babu ko mutum guda da ya tsaira da rai daga cikin mutane 11 dake cikin wannan jirgin sama da ya fadi litinin a Charlesville, mai tazarar kilomita 45 a kudu maso gabas da Monrovia, babban birnin Liberiya.

Manajan kula da ma'aikata na filin jirgin Saman Roberts International dake kusa da nan, Winston Beslow, ya fadawa 'yan jarida cewa an fara gudanar da binciken musabbabin faduwar jirgin.

Wata mace da ta ga faduwar jirgin da idanunta, ta fadawa Muryar Amurka cewa ta ga hayaki da wuta na fita daga jirgin yayin da yake sama.

Tawagar sojojin Guinea, tana kan hanyarta ce ta zuwa bukin ranar sojoji ta kasar Liberiya a birnin Monrovia.

Shugaba Ellen Johnson-Sirleaf ta Liberiya, ta ziyarci inda jirgin ya fadi litinin, ta kuma ayyana talata a zaman ranar makoki a fadin kasar Liberiya.

Gwamnatin Guinea, ta ayyana nzaman makoki na tsawon kwanaki uku, tun daga litinin.

Babban hafsan sojojin kasar Guinea, Janar Souleymane Diallo, na hannun damar shugaba Alpha Conde na kasar ne. Litinin, shugaba Conde ya nada mataimakin Janar Diallo, Janar Namory Traore, da ya rike mukamin babban hafsan sojojin kasar na wucin gadi.
XS
SM
MD
LG