Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Ya Nemi Ayi Taron Duniya Kan Barazanar Duwatsu Daga Samaniya


Hoton wannan dutse lokacin da yayi bindiga wanda wani mutumi ya dauka daga cikin motarsa a kan hanyar zuwa Chelyabinsk, Jumma'a 15 Fabrairu 2013

Gwamnan Chelyabinsk inda wani dutse ya fado ranar Jumma'a yace kasa daya ba zata iya tunkarar irin wannan dutse kio wanda ya fi shi girma ba

Gwamnan yankin Chelyabinsk na kasar Rasha, inda wani dutse daga samaniya ya fado yayi barna mai yawa, ya nemi shugabannin kasashen duniya da su je su yankin nasa domin tattauna yadda duniya zata hada hannu wajen daukar matakan kare irin wannan barazana a nan gaba.

Gwamnan yankin na Chelyabinsk, Mikhail Yurevich, yayi magana ta wayar tarho da ‘yan jarida dake birnin Moscow jiya litinin. Yace babu wata kasar da zata iya kaddamar da tsaro ta sama da ake bukata domin tare irin dutsen da yayi bindiga a daidai kan yankinsa a ranar jumma’a da ta shige, ko kuma wanda ma ya fi shi girma.

Bindigar da wannan dutse yayi a lokacin da ya shigo cikin iskar da ta kewaye duniya a daidai yankin, ta farfasa gilashin tagogin gidaje kusan dubu 5 a garin Chelyabinsk. Mutane fiye da dubu daya sun ji rauni a garin.

Wakilin yankin Chelyabinsk a babbar majalisar dokokin tarayya ta Rasha, Konstantin Tsybko, yace garin Chelyabinsk shi ne na farko a tarihi da ya tsira daga abinda ya kira “farmaki daga sararin samaniya.”

Har yanzu akwai mutanen garin da dama dake asibiti su na jinyar raunukan da suka samu lokacin da wannan dutse ya fado daga samaniya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG