Jami'in ya fada yau laraba cewa shi ma shugaba Obama ya yanke shawarar sadaukar da kai irin wanda ala tilas wasu ma'aikatan gwamnati zasu yi a saboda dokar nan da ta tilasta zabtare kudaden da kowace ma'aikata da hukuma ta gwamnatin tarayya a nan Amurka ta ke kashewa.
Shugaba Obama yana samun albashin Dala dubu 400 a kowace shekara, kafin a cire haraji daga ciki. Kashi biyar na albashin nasa da zai sadaukar daga ranar 1 ga watan Maris, lokacin da wannan doka ta fara aiki, na nufin cewa a kowane wata zai mayar da kimanin dala dubu daya da dari bakwai.
A ranar talata ma, sakataren tsaron Amurka, Chuck Hagel, da mukaddashinsa Ashton Carter, duk sun ce su ma zasu maidawa gwamnatin wani bangare na albashinsu a matsayin wani matakin jajantawa ma'aikatansu da zasu yi hasarar wani bangare na albashinsu.