Accessibility links

An sallami Stella Oduah, da Yerima Ngama, da Godswill Orubebe da kuma Caleb Olubolade, yayin da aka maye gurbinsu da wadanda zasu rike na wani lokaci

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya sallami ministar zirga-zirgar jiragen sama, Stellla Oduah, da ministan harkokin yankin Niger Delta, Godswill Orubebe, da ministan Ayyukan 'Yan sanda, Caleb Olubolade, da kuma karamin ministan harkokin kudi, Yerima Ngama.

Ministan yada labarai, Labaran Maku, yace karamar ministar babban birnin tarayya, Olajumoke Akinjide, ita ce zata rike ma'aikatar 'Yan sanda kafin a nada minista. Karamin ministan cinikayya, Sam Ortom, zai rike ma'aikatar jiragen sama.

Haka kuma, karamin ministan Niger Delta, Gayus Isiyaku, zai rike ma'aikatar kafin a nada mata minista, yayin da ministar harkokin kudi, Ngozi Okonjo-Iweala, zata rike ayyukan karamin ministanta da aka sallama.
XS
SM
MD
LG