Accessibility links

Da Gaske Ne Jonathan Ya Kori Babban Jami’in Ofishinsa?


Shugaba Goodluck Jonathan

Baza a iya tabbatar da cewa an kori Mike Oghiadomhe a matsayinshi na babban jami’in ofishin shugaban kasa, mukamin da ya rika tun lokacin da Shugaba Goodluck Jonathan yake rikon kwaryar shugabancin kasar Najeriya.

Amma ana cewa ya bada sanarwar ajje aiki ne saboda ya shiga al-amuran siyasa ganin cewa makonni biyu da suke wuce, shugaban kasa ya umarci duk wani jami’insa dake son shiga siyasa akan ya ajje aiki.

Amma akwai bayanan dake nuna cewa akwai wasu matsaloli da suka shafi matsala ta zargin hannun shi Mike Oghiadomhe akan maganar kudade na man fetur na miliyan dubu ashirin, badakalar da ake ta kururuwa akai, da kuma magana dake nuna cewa bai aikawa Gwamnan jihar Sokoto Aliyu Magatakarda Wammako wasikar cewa shugaban kasa zai je ziyara a Sokoto, domin karbar tsohon gwamnan jihar Attahiru Baffarawa wanda ya shiga jam’iyyar PDP.

Kafin badakalar kudaden man fetur ta faro, Mr. Mike yana daya daga cikin jami’an da suka nemi a sallame su aiki saboda sa hannu, ko sa baki da kafar ungulu da ake zargi yana yi a wurin gudanar da aikin gwamnati, ko hana gwamnati yin aiki yadda ya kamata a yi, saboda bakinsa.

XS
SM
MD
LG