Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC ta Mayarda Martani Kan Ziyarar Jonathan Zuwa Sokoto


Shugaba Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan

Yayin da ake ganin ziyarar Shugaba Jonathan zuwa Sokto tafi ta karbar Attahiru Bafarawa kawai sai gashi 'yan jam'iyyar APC suna kai ruwa rana kan ziyarar

Karshen makon da ya gabata shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ziyarci Sokoto domin karbar tsohon gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Bafarawa zuwa cikin jam'iyyar PDP.

Da alama manufar taron jam'iyyar PDP da shugaba Goodluck Jonathan ya jagoranta a Sokoto ta wuce ta karbar Attahiru Bafarawa da magoya bayansa kadai domin shugaban ya yi kokarin bayyanawa duniya cewa jam'iyyar tana nan daram da kwarjininta duk da rigingimun da ta sha fama da su tare da ficewar wasu gwamnoni. Shugaban ya ce suna son su yi anfani da jihar Sokoto a zaman misali cewa har yanzu jam'iyyar PDP ita ce mafi yawa da karfi a duk fadin Najeriya.

A cigaba da jawabinsa a Sokoto shugaban kasa ya kaucewa fitowa fili ya fada ko zai sake tsayawa takarar zaben shugaban kasa abun da kowa ke jira ya ji. Sai dai ya ce har yanzu jam'iyyarsa bata tsayar da kowa ba tsayawa zabe. Babu wani dan takara a jam'yyar yanzu.

To sai dai 'yan kasuwar kara da ta kone kwanan nan Allah Ya yi masu gydar dogo domin yayin da shugaban ya ziyarci kasuwar ya basu taimakon nera miliyan 250 kana ya yi masu alkawarin taimako daga gwamnatin tarayya.

To sai dai jam'iyyar adawa ta APC ta mayarda martani kan ziyarar. Ta ce siyasa ce kawai. Shugaban kungiyar matasan 'yan kasuwa ta jihar Sokoto Alhaji Kabiru Hali ya ce an yi gobara a kasuwanni daban daban a cikin Sokoto duk da an sanarda shugaban kasar bai taba zuwa Sokoto ya jajantawa wadan da suka yi asara ko kuma ya aiko da taimako ba.

Duk da cewar APC bata damu da zuwan shugaban ba amma ta fusata da Sanato Muhammed Ahmad Maccido da ya ki bin sawun takwarorinsa wajen komawa APC. Jam'iyyar ta ce ta la'anci sanatan kuma basa tare da shi. Amma Bafarawa ya jinjinawa sanatan da ire-irensa da suka tsaya cikin PDP.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG