Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Sabon Zagayen Rigakafin Cutar Polio A Jihar Neja


an kaddamar da zagaye na biyu na aikin bayar da rigakafin cutar Polio na wannan shekarar a masarautar Lapai

An kaddamar da zagaye na biyu na bayar da maganin rigakafin cutar shan inna, ko Polio, na wannan shekara a jihar Neja, a ci gaba da yunkurin da ake yi na ganin an raba Najeriya da wannan cuta mai nakkasawa ko ma kisa.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da wannan gangami a masarautarsa, mai martaba sarkin lapai, Alhaji Umaru Bago Tafida, ya roki jama'a su bayar da hadin kai ga ma'aikatan kiwon lafiyar domin a kawar da wannan cuta.

Yace ba kuma za a iya kawar da cutar ta shan inna ba, har sai kowa da kowa ya bayar da hadin kai sosai.

Jami'i mai kula da yaki da cutar Polio a Jihar Neja, Dr. Yabagi Aliyu, yace an bayar da horo mai kyau ga ma'aikatan da zasu gudanar da wannan aiki a bangaren yunkurin tabbatar da samun nasararsa.

Yace kamar yadda suka saba, a wannan karon ma zasu yi kokarin gudanar da aikin rigakafi mai inganci domin taimakawa al'ummar jihar.

Alhaji Ahmed Musa Ibeto, mataimakin gwamnan Jihar neja, kuma shugaban Kwamitin yaki da Polio na Jiha, ya ce akwai wasu sassa da dama na jihar da suke da wahalar kaiwa a saboda su na cikin tsaunuka ne ko kuma dai sai ta ruwa kawai ake iya kaiwa cikinsu. Yace a irin wadannan wurare, zasu yi amfani da dabbobi da kuma kafa domin dai a ga cewa babu wanda aka bari a baya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00
Shiga Kai Tsaye

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG