Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar Muhammadu Buhari ya Soki Lamirin Shugaba Goodluck Jonathan


Muhammadu Buhari,

Janar Muhammadu Buhari ya zargi shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da daurewa cin hanci da rashawa gindi

Janar Muhammadu Buhari na jamiyar, APC, ya zargi shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, da daurewa cin hanci da rashawa gindi, da sanya ‘yan kasar cikin mummunar talauci, da kuma gazawa wajen hana kashe-kashe dake afkuwa a Najeriya..

Mai Magana da yawun shugaba Jonathan Ruben Abati, yace wannan zargi da Buhari yayi ba gaskiya bane.

Yace wadannan kalamai, na nuni da cewa irin adawar dake kasar ba adawa bace mai kyau, idan hara shugaba irin janar Buhari, zai yi munanan kalamai don ya jawo ra’ayin, ‘yan kasa su zabe shi.

Ruben Abati, ya kara da cewa sanin kowane a wannan mulkin na Goodluck, an samu ci gaba a fanin tattalin arziki har kashi 6 ko 7 cikin 100, wani abu da yasa Najeriya, akan gaba da sauran kasashen nahiyar Afrika, sannan itace kasa ta 26, a ayarin, kasashe masu karfin arziki, a duniya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG