Accessibility links

Gwamnatin Najeriya Tana Tautaunawa da ‘Yan Kungiyar Boko Haram


Shugaban Chadi Idriss Deby, da Shigaba Najeriya, Goodluck Jonathan 2014.

Ana tautaunawa kan sakin ‘yan matan Chibok sama 200 da’aka sa ce wata shida da suka shude dakuma ganin an sasanta kan hare-hare.

Gwamnatin Najeriya tana tautaunawa da ‘yan kungiyar Boko Haram domin neman ganin an saki ‘yan matan Chibok sama 200 da’aka kame wata shida da suka shude dakuma ganin an sasanta kan hare-haren da suka yi sanadin hallakar dubban rayukan mutane.

Wani mai baiwa shugaban kasar Najeriya Shugaba Goodluck Jonathan shawara da kuma wani mutum daya kira kanshi “Babban Sakataren” kungiyar boko haram sun fadawa sashen Hausa na Muryar Amurka jiya Alhamis cewa ana gudanarda wannan tautaunawar a Saudi Arabia, kuma ta hada da wakilan kasashen Chadi da Cameroon.

Sakataren na ganal kungiyar Boko Haram Danladi Ahmadu, wanda ke Saudiya yanzu haka yace “ ‘yan matam na cikin kwanciyar hankali da koshin lafiya”.

Tun ranar 14 ga watan Afrilu na wanan shekarar ne, ‘yan Boko Haram suka afkawa makarantar sakandaren ‘yan mata ta Chibok inda suka sace kusan yara 270. Sai dai kuma 57 daga cikin ‘yanmatan sun kubuta.

Danladi Ahmadu dai bai tabbatar da abinda suke bukataba kafin sakin ‘yan matan ba.

Haka shima Babban mai baiwa shugaban kasar Najeriya shawara Doyin Ukupe bai tabbatar wa da Muryar Amurka sahihancin wannan tautaunawar ba.

XS
SM
MD
LG