Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Gwamnan Jihar Neja Ya Fito Neman Kujerar Gwamna a Zaben 2015


PDP

Yayin da Janaral Buhari ke bayyana kansa a neman zama dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyarsa a can jihar Neja kuma mataimakin gwamnan ne ya fito neman kujerar gwamna a zaben 2015.

Fitowar mataimakin gwamnan jihar Neja Alhaji Ahmad Musa Ibeto shiga zaben 2015 ta kawo karshen tababar da mutane ke yi sabili da jita-jitar cewa baya samun goyon bayan gwamnan jihar mai ci yanzu Dr Aliyu Babangida.

Daraktan neman zaben mataimakin gwamnan Alhaji Inusa Kasanagi yace suna da kwarin gwiwar samun nasara tun da mulki daga Allah ne. Daga yadda mutane suka fito yayin da suke yankar takardar zaben ya nuna cewa akwai alamar nasara.

Jam'iyyar PDP dama tace duk wani dan jam'iyyarta mai sha'awar neman mukami yana da 'yancin yin hakan ba tare da nuna wariya ba.

Ahalin yanzu mutane bakwai ne ke neman kujerar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP a ciki har da shugaban ma'aikatan gidan gwamnati Alhaji Umar Nasko wanda ake ganin shi ne wanda gwamnan jihar ke marawa baya.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG