Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Jonathan Arewa Maso Gabas Ya Tayar Da Kura


Ziyarar da shugaba Jonathan yakai a wasu yankunan da aka kwato daga hannun yan boko haram ya bar baya da kura.

Domin ko, ko baya ga al’ummomin da aka kwato haka nan masu fashin baki ta harkokin tsaro irin su mallam Mohammed Abdul Hamid na ganin, akwai abin dubawa game da ziyarar da shugaban kasar yakai dangane da wannan lokacin.

Ga dai abinda yake shaidawa wakilin wannan gidan radio, “Tun lokacin da wannan gari na Bobi ya kubbuce daga yan kungiyar ahalil sunna lid di awaiti wal jihad, wato yan boko haram, watanni nawa yanzu amma sai yanzu shugaban kasa yaje, ana cikin watanni na hudu kenan, yaje kawai ya zagaya, yaje ne wai zuwan ma zuwan bazata wanda jamaa ma basu san zaizo ba, yayi dai dai da irin zuwan nan ne da kasashe saboda suma suna tsoron yanayin, sai dira kawai sai dai kawai sai bayan sun tafi sai aji wai sunzo, irin shigar ce yayi.Don haka jamaa talakawa da sauran jamaa gari da ire-irn mu zamu ga cewa da ya damu da al’ummar da tun a lokacin zai yanke abinda yake yi ko bai zo ba da ya wakilta koda mai bashi shawara ne a fannin tsaro yace jeka wannan wuri kaga halin da wadannan jamaa suke ciki, kuma yace me yakamata ayi musu, duk baiyi haka nan ba, sai yanzu kwatsan sai aji shi ya dira ya tafi, kai kasan akwai harshe biyu, akwai nazo neman kuriaar ku, sannan kuma nazo ganin shin yaya lamarin abinda ya samu abokin aiki nawa wato Chief Of Army Staff, wannan a bayyane yake, ko sun karyata ko sun gasganta wannan ba wani abu ne da akayi shi ba domin nuna halin da mutanen mubi suke ciki ba”.

Sai dai kuma a nasu bangaren ofishin kanfe na shugaba Googluck sun mayar da martini inda mataimakin kakakin mai Magana da yawun ofshin kanfe din Yarima Tafidan Muri ke cewa:

“Na farko dai shi shugaban kasa shine kwamanda na gaba daya na sojojin Najeriya kuma sojojin Najeriyan nan suna bukatar a karfafa musu gwiwa, cewa aikin nan da suke yi na kasar Najeriya ne suke yi gaba daya kuma kowa a Najeriya ya gamsu da abinda suke yi’’

Sai dai da kuma da aka tambaye shi amma ana ganin cewa da manufar siyasa da shugaban kasa yakai wannan ziyara a yanzu? Sai ya amsa da cewa

“Ai shugaban kasa ba siyasa kawai yake ba lokacin nan lokacin siyasa ne mun yarda amma wannan zuwa nasa ba yaje wai domin ya nemi kuria bane duk lokacin da shugaban kasa zaiyi wani abu akwai matakan tsaro iri-iri wanda za a kawo masa shawarwari idan sharwari sun gamsu ga mutanen tsaro suka ce sun yarda yaje ba yadda zaiyi ba zaije ba, amma lokacin da suke wannan abun babu tabbas akwai matsala

Sai kuma da aka sake tambayar sa ko yaushe shugaban kasan zaije chibok domin sanin halin da jamaa suke ciki?

“ Zaije duk lokacin da tsaro ya kyautata, yanzu dai wajen chibok yana wurin boko haram lokacin da aka tabbatar tsaro ya kankama ba sai wani ya fada masa ba zaije”

Yankin Mubin da aka kwato yau wajen watanni hudu kenan ne shugaban kasar ya fara ziyarar ba zatan, ga kuma abinda wasu jamaar garin ke cewa

“Munga helikwapta sun kai guda biyu suna shawagi aka Goodluck ne yazo abinda yaba mutane mamaki shine sojoji sun hana mutane fita, sun rurrufe hanyoyi bamu samu mun isa wurin ba domin muji jawabin da yayi’’

Ance yaje kofar Sarki ba a bari kunje kunji jawabin da yayi muku ba?

‘’Yaje ba wanda yasan cewa shugaban kasa zaizo Mubi’’

Ba yazo ya ganinku bane?

‘’Yazo yaga gidan sarki dai domin daga bariki sai kofar Sarki, daga kofar sarki ya sake komawa bariki abinshi sai yayi gaba’’

To yaya kuka ji da zuwan nasa?

‘’Abinda zuwan sa ya bamu mamaki baizo yayi muna jawabi ba kuma bai fada muna sakon da yazo dashi ba, ya ma barmu da zullumi ne’’

Yanzu haka dai sojojin na kara nausawa aka samu ninda nasarar kwatowa.

XS
SM
MD
LG