Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Iran Da Wani Babban Shaihi SUn Yi Tur Da Kashe Kashen Zariya


Dalibai musulmi dauke da kwalaye su na zanga-zangar kashe daruruwan 'yan mazhabin Shi'a da ake zargin sojojin Najeriya da aikatawa a Zariya.
Dalibai musulmi dauke da kwalaye su na zanga-zangar kashe daruruwan 'yan mazhabin Shi'a da ake zargin sojojin Najeriya da aikatawa a Zariya.

Majalisar dokokin ta bada sanarwar yin tur da kashe-kashen yayin da Marja Ayatollah Lotfollah Safi Golpaygani yayi tur da yadda kasashen duniya suka yi shiru kan kashe-kashen

Majalisar dokokin kasar Iran ta bayar da sanarwa a yau talata tana yin tur da kashe "daruruwan" 'yan mazhabin Shi'a da sojojin Najeriya suka yi a garin Zariya dake Jihar Kaduna a arewacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran, IRNA, ya ce a lokacin da aka bude zaman majalisar a yau talata, wakilai 214 daga cikin wakilai 290 na majalisar sun dora laifin tashe-tashen hankulan a kan sojojin Najeriya.

'Yan majalisar dokokin ta Najeriya sun yi kira ga shugaban Najeriya da ya kafa wani kwamiti na musamman da zai binciko wannan lamarin.

Wannan yana zuwa a daidai lokacin da daya daga cikin manyan shaihunan malaman Shi'a na duniya, babban Ayatollah Lotfollah Safi Golpaygani, yake nuna matukar damuwa da kashe-kashen tare da yin kira ga hukumomi na duniya da su yi tur da irin wadannan kashe kashen.

Marja Ayatollah Golpaygani yace maimakon su maida hankulansu wajen kashe 'yan ta'addar Boko Haram, sojojin Najeriya sun gwammace su kashe 'yan Shi'a dake fuskantar danniya, kuma ba su yin barazana ga wata kasa ba.

Har yanzu dai ba a ji ta bakin hukumomin Najeriya a kan wannan suka ta kasar Iran ba.

XS
SM
MD
LG