Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Wani Salon Yaki Da 'Yan Boko Haram Akan Babura


Sojojin Najeriya a jikin baburan da zasu rika shiga daji da su wajen yakar 'yan Boko Haram
Sojojin Najeriya a jikin baburan da zasu rika shiga daji da su wajen yakar 'yan Boko Haram

Amurka zata tura dakarunta domin samar da horo ga dakarun Sojojin Najeriya, ta yarda zasu murkushe ‘yan Boko Haram,

Rundunar Sojojin Amurka zata tura dakarunta domin samar da horo ga dakarun Sojojin Najeriya, ta yarda zasu murkushe ‘yan Boko Haram, a shiyar arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin hedkwatar rundunar Sojojin Najeriya Birgediya janar Rabe Abubakar, yace yaki da ta’addanci ba yaki bane na kasa

Daya har mayan kasashe na duniya na kai dauki ga kasashen dake fuskatar kalubale na ta’addanci.

Ya kara da cewa yaki da ta’addanci kalubale ne ga kasashen duniya bawai kasa daya ba, saboda har idan Amurka ta kawo dauki da duk masu son taimakawa toh lalle Najeriya na maraba dasu.

A gefe daya kuma rudunar Sojan ta Najeriya ta kaddamar da Birged guda na mayaka akan Babura a yankin na arewa maso gabas.

Shi dai babban hafsan sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai ya sha damarar raba yankin na arewa maso gabas da ‘yan ta’adda na Boko Haram.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG