Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Ya Kara Fadada Tazarar Da Ya Baiwa Abokan Hamayyarsa


Sanata Bernie Sanders da ya fito daga Jihar Vermont ya samu nasarar bazata

Sanata Bernie Sanders da ya fito daga Jihar Vermont ya samu nasarar bazata a zaben fidda gwani da aka yi na ‘yan takarar neman shugabancin Amurka a jihar Michigan da ke a karkashin jam’iyyar Democrat.

Shi kuwa mai neman takarar a karkashin jam’iyyar Republican, Donald Trump ya kara fadada tazarar da ya baiwa abokanan hamayyarsa a jihar ta Michigan da Misissipi da kuma Hawaii a zaben da aka yi a jiya Talata.

Kuri’ar neman jin ra’ayin mutane da aka gudanar da dama gabanin wadannan zabuka, sun nuna cewa Hillary Clinton ce za ta lashe Michigan, amma sai ga shi Sanders ne ya lashe zaben.

Sai dai Clinton ta samu nasarar lashe zaben Misissipi cikin ruwan sanyi.

Yayin da ya ke jawabi, Sanders ya ce wannan nasara da ya samu alama ce da ke nuna cewa sauyin da ya ke so ya samar a fannin siyasar kasar na karbuwa a wajen Amurkawa.

Ya kuma kara da cewa har yanzu ba a je yankunan da ya fi karbuwa a zabukan fidda gwanin da ake yi ba.

Ita kuwa Clinton ta gayawa magoya bayanta cewa, tana mai alfahri da irin yakin neman zaben da suke yi tare da Sanders idan aka kwatanta da na takwarorinsu a jam’iyyar Repblican da ke sukar junansu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG