Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatar Tsaron Rasha, Ta ce Wasu Karin Jiragen Kasar Na Ci Gaba Da Janyewa Daga Syria


Sakataren harkokin wajen Amurka na shirin kai ziyara birnin Moscow a mako mai zuwa domin ganawa da shugaba Vladimir Putin

Ma’aikatar tsaron Rasha, ta ce wasu karin jiragen kasar na ci gaba da janyewa daga Syria a yau Laraba, wanda hakan ke kara nuna alkiblar da Rashan ta dauka na janye dakarunta daga kasar ta Syria.

Hakan na faruwa ne yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke ci gaba da jagorantar wata tattauna ta bayan fage tsakanin bangarorin da ke yaki da juna. Ana kuma zaman ne a birnin Geneva.

Sakataren harkokin wajen Amurka na shirin kai ziyara birnin Moscow a mako mai zuwa domin ganawa da shugaba Vladimir Putin, kan makomar yunkurin da ake yi na samar da zaman lafiya a kasar.

Kerry ya kara da cewa bayan ganawa da zai yi da shugaba Putin, zai kuma tattauna da takwaran aikinsa Sergie Lavrov, domin neman maslaha ga rikicin na Syria da aka kwashe shekaru biyar ana yi.

An dai samu raguwar tashin hankali matuka a kasar ta Syria, yayin da ake cin moriyar shirin tsagaita wutar da aka cimma ta tsawon makwanni uku.

A kuma cewar Kerry, yanzu ne ya kamata a yi amfani da wannan dama domin cimma bukatun da ake so a cimma wajen kawo karshen rikicin.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG