Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Taka Rawar Gani Wajen Yaki Da Boko Haram


Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Yada Labarai ta Amurka, John Lansing, yana maraba da ministan tsaron Najeriya, Janar Mansur M. Dan Alli, a ofishinsa a Washington

Ministan tsaro na Najeriya Mansur Dan Ali yace sojoji karkashin mulkin shugaba Muhammadiu Buhari sun takarawar gani a yaki da Boko haram.

Janar Dan Ali mai ritaya ya fada yau laraba cewa sojojin sun samu nasarar kwato kusan dukkan wuraren da wannan kungiya ta Boko haram ta karbe a wani lokaci can baya. Yace ‘yanzu an bar kungiyar da kai hare haren irin na sari ka-noke.

Yace ta samu wannan nasarar ce a cikin kasa da shekara daya da shugaba Muhammadu Buhari ya kama ragamar mulki.

Janar Dan Ali yace dubi abinda ya faru da, inda jihohi ukku na arewa maso gabas ada duk suna karkashin wadannan ‘yan taaddan ne amma yau kila ace kananan hukumomi biyu suka rage ba a kammala kakkabe wadannan yan kungiyar ba.

Yace haka kuma sojojin zasu tabbatar sun gama kakkabe sauran ‘yan boko haram din da suka rage a cikin dajin sambisa cikin watanni biyu zuwa ukku.

Ministan yace jim kadan da kaddamar da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a cikin watan maris na shekarar 2015 yace yana da kwarin gwiwa za a fatattaki yan boko haram zuwa karshen shekara, kuma hakan ta faru domin zuwa karshen shekarar ce Shugaba Buhari yace an gama da wannan kungiyar abinda ya rage shine sharar fili.

XS
SM
MD
LG