Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram nada karfi a wasu sassan jihar Borno


Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima wanda aka ce kungiyar Boko Haram nada karfi da kuma yawa a wasu sassan jihar.

Kimanin mutane miliyan daya da dubu dari tara ne suka rasa matsugunansu sakamakon hare haren kungiyar Boko Haram a Najeriya. Galibi suna zaune a sansanin ‘yan gudun hijira ko kuma gidaje dake fama da cunkoso a duk fadin kasar. Gwamnati tace tana shirin ginawa jama’a gidaje. Sai dai da dama suna ganin kamar ba zasu ga wannan ranar ba.

Wakilin Muryar Amurka Chris Stein ya aiko rahoto daga Maiduguri inda ya yi hira da John ali, wani da ya kauracewa gidansa a kauyen Gwoza lokacin da kungiyar Boko Haram ta kai hari, shekaru biyu da suka shige, kuma har yanzu yana zaune a wani sansani dake wani wuri kusa da Maiduguri,

Yace,har yau, ‘yan kungiyar Boko Haram suna da yawa. Suna da karfi. Har sun kafa sansani a kauyenmu. saboda haka babu yadda mu koma ba. Amma muna son komawa.

Kungiyar ta lalata kimanin gidaje miliyan daya da sama da azuzuwa dubu biyar, bisa ga cewar gwamnati.

Cibiyar agajin gaggawa ta kasa tana so ta fara maida mutane gidajensu bana, sai dai kakakin cibiyar yace suna jira rundunar soji ta tabbatar babu sauran barazanar tsaro

Kwananan aka bude hanyar da ta hada babban birnin jihar da garin Damboa,da sojoji suka ce bata da wani hatsari, sai dai, farin kaya sukan jira ayarin sojoji ya raka su zuwa kudancin jihar.

XS
SM
MD
LG