Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sandan Faransa Sun Yi Amfani Da Barkonon Tsohuwar Akan Masu Zanga-Zanga


Akalla ‘yan gudun hijira 150 ne suka mamaye makarantar Jean Jaures

‘Yan sandan Faransa sun yi amfani da barkonon tsohuwar akan masu zanga-zanga yayinda jami’ai ke kwashe ‘yan gudun hijira daga wata makarantu a birnin Paris, inda suka fake makonni da yawa da suka wuce.

Akalla ‘yan gudun hijira 150 ne suka mamaye makarantar Jean Jaures dake arewa maso gabashin birnin Paris a lokacin da ake gyaran makarantar. A yau laraba ne ‘yan sanda suka je makarantar suka kuma tilsta masu tashi. Wadanda ke cikin ginin makarantar sun toshe kofofinta yayinda masu zanga-zanga su ka nemi su hana kowa shiga daga waje.

Shugaban 'yansandan birnin na Paris, Michel Cadot, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labara AP cewa jami’an tsaro sunyi amfani da barkonon tsohuwar don korar masu zanga-zangar da ke kan hanyarsu.

Cadot ya ce a kwashe ‘yan gudun hijirar zuwa wasu cibiyoyi kuma an basu shawarar su neman alfarmar mafakar zama a kasar.

A halin da ake ciki kuma, ta yiwu a tilastawa kasashen tarayyar Turai su biya tara in har suka ki yarda su karbi ‘yan gudun hijirar da suka kwararo cikin nahiyar, suna neman mafaka.

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG