Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiya Ta Kakkabo Wani Makami Mai Linzami Daga Yemen


FILE - makami mai linzami
FILE - makami mai linzami

Kasar Saudiya tace ta kakkabo wani harsashi mai linzami da aka harbo daga Yemen jiya Litinin da dare.

An lalata harsashin mai linzami ne a sararin sama ba tare da cutar da kowa ba, bisa ga cewar kamfanin dillancin labaran kasar Saudiya SPA. Wannan ne harsashi mai linzami na biyu da Saudiya a kakkkabo da Yemen ta harbor cikin wataguda.

Dakarun hadin gwiwa da Saudiya ke jagoranta, dake goyon bayan shugaban kasar Yemen Abdu Rabu Mansour Hadi, tace wannan harin na iya sawa su sake shawara a kan tsagaita wutar da aka yi da ta bada damar tattaunawar wanzar da zaman lafiya karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya a Kuwait cikin watan Afrilu.

‘Yan tawayen Houthi ke iko da Sa’a babban birnin kasar tunda suka kwace shi a watan Satumba shekara ta dubu biyu da goma sha hudu. Bayan watanni shida, suka doshi kudancin kasar da gumurzun da ya kai ga kwace tashar sufurin ruwa dake birnin Aden, da kuma tilastawa shugaban kasar Hadi, gudu zuwa Saudiya.

Tuni gwamnatin Hadi ta sake kwace Aden, tare da taimakon dakarun hadin guiwa karkashin jagorancin kasar Saudiya. Rikicin ya yi sanadin kashe mutane dubu shida da dari hudu, miliyoyi kuma suna matukar bukatar agaji.

XS
SM
MD
LG