Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi Gwamnatin Gambiya Da Sauya Ma Fursunonin Siyasa Matsuguni


Shugaba Yahya Jammeh

A watan da ya shige, an kama mutane 38, cikinsu har da shugaban jam’iyyar UDP, Ousainou Darbo

Jam’iyyar adawa ta UDP a kasar Gambiya ta yi zargin cewa gwamnati ta sauya ma wasu fursunonin siyasa matsuguni zuwa wani wurin da ba a sani ba.

A watan da ya shige, an kama mutane 38, cikinsu har da shugaban jam’iyyar UDP, Ousainou Darbo, aka tuhume su da hada baki domin aikata laifi a bayan da suka yi zanga-zangar nuna Rashin jin dadin mutuwar wani jami’in UDP, Solo Sandeng, a hannun hukuma. Haka kuma sun bukaci da a aiwatar da sauye sauyen siyasa.

Shugaban kwamitin yada labarai na magoya bayan jam’iyyar UDP a kasashen waje, Karamba Touray, yace jam’iyyarsu tana dora ma gwamnati alhakin duk wani abinda zai samu wadannan mutane da ta kama take tsare da su.

Ya zargi gwamnatin da cewa ta yi kaurin suna wajen take dokokin kasar, musamman ma yadda mutane suke bacewa a hannun ‘yan sanda.

XS
SM
MD
LG