Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Alaka Tsakanin Shan Ruwa Ko Shayi Mai Zafi Da Kamuwa Da Cutar Sankara


Ban Ki-moon
Ban Ki-moon

A yanzu, an sanya shan shayi ko gahawa mai zafi, ko wani ruwa mai zafi a cikin jerin abubuwa da ka iya haddasa cutar sankara.

Wani sabon nazarin da cibiyar binciken cutar sankara ta Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar ya nuna cewa akwai alaka a tsakanin shan ruwa ko shayi mai zafi da kamuwa da cutar sankara.

Hukumar Binciken Cutar Sankara ta Duniya wadda take zaman bangaren Hukumar Kiwon lafiya ta Duniya, ta fada yau laraba cewa akwai shaidar cewa idan aka sha ruwa ko wani abu makamancinsa mai zafin akalla digiri 65 a ma’aunin Celsius, zai iya janyo cutar sankarar makogwaro.

Wannan ya biyo bayan nazarin da aka gudanar a kasashen Iran, China da kasashen Amurka ta Kudu inda aka saba shan shayi ko gahawa mai zafin Celsius 70 ko fiye da haka.

A kasashen da suka ci gaba, abubuwan dake haddasa cutar sankarar makogwaro sun hada da shan taba sigari ko shan barasa, amma irin wannan cutar ta fi yawa a sassan duniya inda ake shan abu mai zafi sosai.

A yanzu, an sanya shan shayi ko gahawa mai zafi, ko wani ruwa mai zafi a cikin jerin abubuwa kamar dalma, ko fetur ko hayakin injuna a zaman abubuwan da ka iya haddasa cutar sankara.

XS
SM
MD
LG