Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Majalisar Wakilan Amurka Sun Yi Zanga Zanga


Yan jam’iyar Democrat sun bukaci a jefa kuria akan matakin fadada binciken mutum kafin a sayar masa da bindiga

Yau Laraba yan Majalisar wakilan Amirka. 'Yan jam’iyar Democrat kimamin talatin suka yi zaman dirshan na ba zato ko kuma ba saban ba a zauren Majalisar domin nuna rashin amincewar su ga kiyawar da ‘yan jam’iyar Republican suka yi na jefa kuri’a akan gitta tsauraran matakan sayen bindiga, a sakamakon kashe mutane da wani dan bindiga yayi a kwanan nan.

Yan Majalisar yan tawayen sunyi jerin gwano a harabar Majalisar wakilai suka bada sanarwar cewa suna zanga zangar ce domin matsawa kakakin Majalisar Paul Ryan lambar ganin Majalisar zata ci gaba da zama, domin yin muhawara akan wannan batu.

Yan jam’iyar Democrat din sun bukaci Majalisa tayi muhawara sa’anan ta jefa kuria akan wannan matakin fadada binciken mutum kafin a sayar masa da bindiga. Suna son a dauki wannan mataki ne domin hana

wadanda ake zaton yan ta’ada ne samun sukunin sayen bindiga.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG