Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yankewa Oscar Pistorius Hukuncin Daurin Shekaru Shidda


Oscar Pistorius

A yayinda ta ke yanke wannan hukunci, mai shari’a Thokozile Masipe tayi misali da takaicin da Pistorius ya nuna a lokacinda yake wa’adin hukuncin farko

Yau Laraba aka yankewa dan wasa Olympic na kasar Afrika ta kudu, Oscar Pistorius hukuncin daurin shekaru shidda, a saboda an same shi da laifin kashe budurwar sa Reeva Sheenkamp shekaru uku da suka shige.

A yayinda ta ke yanke wannan hukunci, mai shari’a Thokozile Masipe tayi misali da taksicin da shi Pistorius ya nuna a lokacinda yake wa’adin hukuncin farko da aka yanke masa.

A lokacin da ake yi masa shari’a Pitorius yayi ikirarin cewa yayi kuskure ne a lokacinda ya harbe budurwar sa domin ya zaci barwo ne ya shiga gidan sa. Ya harbe ta sau hudu a shekara ta dubu biyu da goma sha uku.

To amma lauyoyin gwamnati sun ce dama ya shirya kashe ta ne.

XS
SM
MD
LG