Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Kasashen Rasha da Siriya Basu Kai Hari Kan Aleppo Ba cikin Mako Daya


Wani shagon sayar da kayan lambu a Aleppo wanda babu komi cikinsa

Kasar Rasha ta fada yau Talata cewa dakarunta da na Siriya basu kai farmaki ta sama ba akan birnin Aleppo dake Siriya cikin kwanaki 7 da suka wuce.

Mai magana da yawun dakarun kasar Igor Konashenkov ya fadi cewa babu jiragen saman yakin Siriya ko na Rasha da suka je kusa da birnin da yaki ya daidaita kuma yake bukatar taimakon agaji cikin gaggawa ga dubun dubatan mutanen da ke birnin.

Konashenkov ya kara da cewa har yanzu hanyoyin agaji 6 suna nan bude ga mutanen da ke so su fita daga yankin birnin na Aleppo da ‘yan tawaye suka mamaye.

A cikin kwanakin 7 harda kwanaki ukun da aka mutunta shirin tsagaita wuta wadda ya kare ranar Asabar din da ta gabata. Kungiyar dake kare hakkin BIl'Adama a Syria mai cibiya a Ingila, ta fadi cewa an kai hare-hare ta sama a Aleppo jim kadan bayan da yarjejeniyar tsagaita wutar ta kare.

Rasha da Siriya kuma sun yi zargin cewa ‘yan tawayen sun hana mutane yin amfani da hanyoyin don fita daga birnin, yayinda su kuma shugabannin ‘yan tawayen suka ce yawancin fararen hula ba sa son fita ne saboda basu yarda da gwamnatin Siriya ba da ma abinda ka iya biyo baya in suka fita.

XS
SM
MD
LG