Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Sama da Dari Biyu Ne Suka Nitse A Tekun Lybia


Wadanda suka tsira daga hadarin jirgin ruwan da ya nitse a tekun Lybia

Wasu mutane da suka kubuta a wasu haduran jirgin ruwa sun shaidawa MDD cewar sama da bakin haure 200 suka nitse a lokacinda wasu jiragen ruwa biyu suka nutsea gabar tekun Lybia.

Wasu daga cikin wadanda suka tsiran sun isa kasar Italiya jiya ranar Alhamis kuma sun ce jirgin ruwan nasu da ya debo mutane sama da dari, ya kife ne sa’o’I kadan bayan ya baro Lybia, a cewar Carlotta Sami, mai magana da yawun hukumar yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ko MDD.

An tsamo wasu mata biyu da da ransu daga cikin tekun, kuma sun shaidawa masu aikin ceton cewar suna cikin wani jirgin ruwa na dabam ne wanda ke dauke da mutane kimanin 120.

Ana kyautata zaton akasarin mutanen dake cikin jiragen ruwa duk ‘yan kasashen Afrika ne.

A cewar kampanin dillancin labarai na Reuters, an tsamo gawarwaki 12 ciki har da jarirai uku.

Wannan hadarin na baya-bayan nan ya kawo adadin rayukan da suka salwanta a tekun Meditareniya zuwa 4, 220 a wannan sheakarar 2016. A shekarar da ta gabata ta 2015,jimillar mutane 3,777 suka mutu a cikin tekun ta Mediterranean.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG